(ABNA24.com) Majiyar sojan kasar ta Libya ta sanar a yau Lahadi cewa; jiragen samanta na yaki sun kai farmaki har sau uku akan sansanin da mayakan Halifa Haftar su ke amfani da shi a yammacin birnin Tripoli.
Kakakin sojan gwamnatin Libya mai matsuguni a birnin Tripoli wacce kuma duniya ta amince da ita, Muhammad Qununu ne ya wallafa wannan labarin a shafinsa na Facebook a yau Lahadi
Bugu da kari Qununu ya ce; Sojojin nasu sun yi amfani da manyan bindigogi wajen kai hari akan wani sansanin na mayakan Haftar da ke yankin Khallatu Bin Aun, a kudancin Tripoli
A ranar Larabar da ta wuce ne dai Janar Halifa Haftar ya sanar da yin watsi da yarjejeniyar Shkhairat wacce dukkanin bangarori da suke fada da juna su ka rattabawa hannu a shekarun baya a kasar Moroko.
Bugu da kari, Janar Halifa Haftar ya nada kansa a matsayin shugaban kasar ta Libya.
/129
4 Mayu 2020 - 03:41
Lambar labari: 1033093
Majiyar sojan kasar ta Libya ta sanar a yau Lahadi cewa; jiragen samanta na yaki sun kai farmaki har sau uku akan sansanin da mayakan Halifa Haftar su ke amfani da shi a yammacin birnin Tripoli.